Tubabbun yan Kungiyar Boko Haram 603 zasu koma cikin al’umma bayan kammala horon sanin Rayuwa

Shalkwatar hukumar tsaro a Nigeria ta bayyana cewa zuwa yanzu tubabbun yan Kungiyar Boko Haram dari shida da uku ne suka 603 suka kammala samun nutsuwar da zasu koma cikin al’umma domin cigaba da rayuwa kamar sauran mutane, Ko’odinatan Hukumar tsaro a bangaren yada labarai John Enenche shine ya bayyana hakan a wajen taron da aka gabatar domin sanar da duniya ayyukan da hukumar Tsaro ke gabatarwa, ranar alhamis a birnin Abuja..

Ya kara da cewa a watan July mai zuwa ake sa ran zaa sallami Tubabbun tare da mayar dasu cikin al’umma, tunda sun samu cikekken horon daya canza tunaninsa tare da yadda suke kallon rayuwa acan baya…

Manjo janar Enenche ya cigaba da cewa shirin da aka tsara a shekarar 2016 mai taken DRR PROGRAMME wanda ke aiki a karkashin hukumar tsaro ya samu babbar nasarar canza tunanin yan Kungiyar Boko Haram da aka kama, inda har aka samu nasarar mayar da yan Kungiyar su 280 zuwa cikin al’umma kuma suke rayuwa lami lafiya da sauran mutane..

Yanzu haka yan Kungiyar Boko Haram dari shida da uku ne ke cigaba da daukar horon sanin rayuwa tare da koyon sana’oi ta cikin DRR PROGRAMME wanda sune zasu kammala horo tare da sallamarsu a watan july…

Abun shaawa ma shine daya daga cikin tubabbun yan Kungiyar daya dauki darasi a hannun jami’an tsaro har ma ya koyi sana’ar Aski yanzu haka yana zaune a garin Bama inda yake cigaba da sana’a har ma ya koyawa wasu mutum hudu sana’ar askin, kuma yake zaune lafiya har ma yayi aure ya fara tara iyali…

Manjo janar Enenche yace an tsara wannam shirin ne domin horar da yan Kungiyar Boko Haram da suka ajiye makamai kuma suke da burin sake komawa cikin al’umma, sune ake basu horon tare da koya musu sana’oi don su dinga samun kudaden tafiyar da rayuwa kamar dai sauran mutane maau son zaman lafiya…

A karshe Manjo Janar yayi kira ga al’umma akan kada su amince da farfaganda da ake yadawa akan tubabbun, sannan yace wannan shirin na daga cikin tsarin da akayi na kawar da masu tayar da kayar baya, da kuma samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas da kasa baki daya…

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*