Saudi Arabia tayi Allah wadai da harin Taadancin da akayi a Arewacin Nigeria

Daular Musulunci ta Saudia tayi Allah wadai da kashe kashen da akayi a Arewacin Nigeria.

Hadiman Masallacin Makka da Madina Mai Martaba King Salman da Yarima Muhammad Bin Salmam sun mika sakon jaje da taaziyya ga shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria akan kashe mutane da yan Kungiyar Boko Haram sukayi a yankin Arewacin Nigeria

Cikin sakon jajen Sarki Salman ya nuna bacin ransa da damuwa tare da bayyana cewa kasar Saudi Arabia tana tare da Gwamnatin Nigeria tare da al’ummarta, shima yarima Muhammad Bin Salman ya aike da nasa sakon na jaje tare da taaziyya ga shugaba Buhari da al’ummar Arewacin Nigeria

Kasar Saudia na tare da Nigeria a lokacin dadi da lokaci mai tsanani irin wannan da yan tayar da kayar baya suke kashe al’umma haka kawai, kuma saudia tayi Allah wadai da halayyar taadanci, tayi adduar Allah ya jikan wadanda suka rasu, wadanda suka samu raunuka Allah ya basu lafiya…

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*