Majalisa ta Amincewa Shugaba Buhari ya karbo Bashin sama da Dollar Biliyan Biyar

A yau laraba zauren Majalisar wakilai ya amince da kudirin shugaba Buhari na karbo bashin sama da Dollar Biliyan Biyar daga waje, a satin daya gabata ne shugaban ya tura majalisar yana neman ta sahale masa ya amso kudaden don gudanar da wasu ayyukan da suka shafi bangaren Coronavirus a Nigeria da wasu abubuwan daban…

Sai dai Majalisar ta kara da wasu Dollar Biliyan hudu da suka nemi shugaban ya karbo, wadanda suka ce ya kamata ayi amfani dasu wajen kyautata jin dadin Maaikata lafiya dake kulawa da annobar Coronavirus, wanda yawan bashin da suka amince a karbo ya koma sama da Dollar Biliyan Goma kenan…

Dama dai a baya kadan zauren sun amincewa shugana buhari daya karbo bashin sama da Dollar Biliyan 22 da wasu kudaden da yawansu ya haura Naira Biliyan dari takwas da duk aka amincewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta amso…

Yanzu dai majalisoshi sun gama nasu aikin na amincewa shugaban daya karbo kudade, shine kawai ya rage daya tura a karbo yayin da al’ummar kasa zasu zuba idanun ganin basukan sun kawo garesu domin kara inganta rayuwarsu..

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*