KORONA: Ko Kasan Inda Za’a Buga Wasan Karshe Na Champions League Din Bana?

Ana tunanin birnin Lisbon na kasar Portugal ya karbi bakuncin wasan karshe na cin kofin zakarun turai wato Champions League na bana cikin watan Agusta, idan hukumar kwallon Turai ta amince.

Hukumar Uefa dai na shirin dauke wasan karshe na Champions League da ya kamata a buga a birnin Istanbul na kasar Turkey da aka tsara yi tun 30 ga watan Mayu, wanda aka sake masa fasali.

Haka kuma hukumar na son dauke karawar karshe a Europa League da aka so yi a kasar Poland ranar 27 ga watan Mayu ta mai da shi zuwa kasarJamus.

Uefa na son buga wasan daf da na kusa da na karshe da na daf da karshe da na karshe a fili daya ba tare da ‘yan kallo ba.

Cikin watan Maris aka dakatar da wasannin cin kofin Zaakarun Turai saboda tsoron yada cutar korona.

Ranar 17 ga watan Yuni ne babban kwamitin amintattu na hukumar kwallon kafar Turai zai yanke hukunci.

Za a buga wasan karshe a gasar Champions League ranar 23 ga watan Agusta, yayin da za a karkare gasar kofin Europa League ranar 21 ga watan na Agusta.

Birnin Lisbon na Portugal yana da manyan filin wasanni biyu da dukkan abubuwan da ake bukata wajen buga wasa da kuma otal da zai dauki kungiyoyin takwas da za su kara a gasar.

A kwanakin baya shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai, Alexandre Ceferin ya tabbatar da cewa hukumar tana iya kokarinta wajen ganin an kammala kakar wasan bana sai dai wasannin babu ‘yan kallo za’a buga su. 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*