Gwamnatin Kano ta Kaddamar da Rabon kayayyakin Lafiya ga Asibitocin Kano

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR, Ya Jagoranci Kaddamar da rabon kayan kwon Lafiya na kimanin miliyan dari tara N900 Million wanda za’a rabasu a dukkan kananu da manyan asibitocin Jihar Kano dake fadin Kananan Hukumomi 44.

Kayayyakin da suka hada da kayyakin haihuwa na mata da magunguna da kayayyakin kariyar jiki na maaikatan lafiya wanda Gwamnatin Jiha da hadin gwiwar Kungiyoyin lafiya na duniya suka bayar.

Yayin da yake kaddamar da rabon kayan a wajen ajiyar kayayyakin lafiya na Rangaza dake karamar hukumar Ungoggo Ganduje ya bukaci dukkan maaikatan lafiya dasu koma bakin aikin su kain da nain su kuma guji rashin bawa marasa lafiya kulawa yayin aikin nasu.

Gwamna yasamu rakiyar Mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna, Kwamishinan Lafiya Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa dana Yada Labarai Malam Muhammad Garba da masu bawa Gwamna Shawara. Yau,Talata. 9/6/2020

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*