FYADE: Kotu Ta Saki Yarinyar Da Ta Kashe Wanda Yayi Niyyar Yi Mata Fyade

Wata kotu a garin Yaba dake jihar legas ta saki wata yarinya ‘Yar shekara 15 wadda take aji uku a babbar sakandire wadda ta kashe wani Dan shekara 51, mai suna Babatunde Ishola, Wanda ake zargin yayi kokarin yi mata fyade.

Mai shari’a Philip Adebowale Ojo ne ya kori karar da aka kai yarinyar, wadda aka boye sunanta bayan da ‘yan sanda suka gurfanar da ita a gaban kotu bisa zargin kisan kai.

Daraktan hukumar kare hakkin al’umma na jihar, Dr. Babajide Martins, Wanda ofishinsa ya tsayawa yarinyar a kyauta, ya bayyana farin cikinsa bisa hukuncin da kotun ta yanke.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*