COVID-19!!! Gwamna Ganduje ya Kaddamar da Gwajin Coronavirus Gida Gida a Kano

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya Jagoranci Kaddamar da gwajin cutar coronavirus gida gida domin cigaba da gwada mutane dake unguwanni don kaucewa yaduwar cutar a fadin Jihar Kano wanda aka gabatar a unguwar Wambai dake Dorayi Babba.

A Jawabin Mai Girma Gwamnan ya tabbatar da Nasarar yaki da cutar a Jihar Kano wanda hakan ze kawo karshen cutar bada dadewa ba insha Allah.

Gwamna yasamu rakiyar Mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna, Kwamishinonin Lafiya, Muhalli, Yada Labarai da masu bawa Gwamna Shawara. Yau,Alhamis. 11/6/2020

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*