Kungiyar Yarabawa Zallah ta Amotekun zata fara Daukar Yan Banga.

Kungiyar tsaro ta yarabawa zallah da ake cece kuce akanta, ta bayyana shirinta na fara daukar yan Banga da zasuyi aikin samar.da tsaro ga yankunan Yarabawa a ranar 19 ga wannan watan na June…

Shugaban Kungiyar na jihar Ondo Chief Adetunji Olu-Adeleye shine ya bayyana hakan ga manema labarai, inda yace dukkan yarabawa suna damar samun aiki a Kungiyar Amotuken, abun da kawai ake bukata shine ya kasance wanda zai shiga yana shaidar karatu koda ta Primary ce, sannan shekarunsa sukai 18 zuwa 70…

Online zaa sauke takardar neman shiga aikin, sannan a cike a sake mayarwa inda aka ciro, kuma kyauta ne Form din, ba sai an biya ko sisi ba…

A baya dai Gwamnatin tarayya ta bakin Babban atoni janar ya bayyana cewa ayyukan Kungiyar harantacce ne, domin babu damar aiwatar da hakan a cikin kundin dokokin Nigeria…

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*